Ministan gida Babatunde Fashola a taron da suka gudanar a jihar Legas ya shawarci ‘yan Najeriya kan yadda zasu kada kuru’unsu a zaben shekarar 2023.
Ministan a batunsa bai ambaci sunan wani dan takara ba yayin da yake shawartar al’ummar Najeriyar,
Amma sai dai yace kar suyi zabe da fushin wani a ransu, suyi zaben bisa cancanta da kuma duba abinda dan takara ya yiwa kasa a baya domin irin sube zasu taimakawa kasa.