Shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, aikin tsaro bana jami’an tsaro bane kadai.
Adamu yace idan mutane suka ga wani abu da basu gane ba ya kamata su rika kaiwa jami’an tsaro rahoto.
Yace sai an hada hannu tare an taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri sannan za’a iya magance matsalar tsaro.