fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ku zo ku zuba jari a kasarmu, akwai zaman lafiya>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan kasuwa na kasar waje

Gwamnatin tarayya ta bayyanawa ‘yan kasuwa na kasar waje cewa su zo su zuba jari a Najeriya kudinsu ba zasu salwanta ba.

 

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka.

 

Inda yace yawancin labaran karyar da ake yadawa na munanan labarai akan Najariya, ‘yan Adawa ne suke yinsu.

 

Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi na masu zuba jari a Legas.

 

Yace cewar da ake wai Najariya ta koma wani fagen yaki ko kuma ana muzgunawa wasu masu addini karyane.

Leave a Reply

Your email address will not be published.