Ministan Kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa, Najariya ta talauce.
Ya bayyana hakane a wajan taron ranar yaki da bautar da kananan yara ta Duniya.
Yace gwamnatin tarayya bata da kudaden da zata gudanar da ayyukan ci gaban kasa a shekara me zuwa wanda hakan zai kara talauci da rashin aikin yi.
Ya bayar da misalin cewa, a baya dala tana 500, ta zo ta koma 600, yanzu ta sake komawa 700.
Yace a yanzu kamfanin mai na kasa, NNPC baya baiwa Gwamnatin tarayya kudin shiga. Yace kudaden da aka karba daga hukumar Kwastam, Haraji, da sauran wasu bangarori ne ake rabawa jihohi.
Yayi kiran cewa, ‘yan Najariya masu kishin kasa su zo a hada kai.