Kudin attajirin Duniya, Aliko Dangote su karu sosai, a yanzu shine na 72 a Duniya da yafi kowa kudi.
Jaridar Bloomberg dake saka ido kan masu kudin Duniya ce ta bayyana haka.
Jaridar tace a yanzu yawan kudin Dangote sun kai da Biliyan $20.4.
Shekaru 11 dai kenan Dangote na rike da kambun wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika.
Hakanan shine bakar fatar da yafi kowane bakar fata kudi a Duniya.
Dangote ya zarta tsohon me kungiyar Chelsea dan kasar Rasha watau Roman Abramovich kudi inda a yanzu shi yake matsayi na 132 cikin masu kudin Duniya.