fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Kudin da ake zargin Abacha da sacewa, Saddam Hussein da Gaddafi ne suka bashi shawarar yawa Najeriya tari>>Buba Galadima

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa kudin da ake zargin tsohon shugaban kasa,Marigayi, Janar Sani Abacha da sacewa wanda ake ta dawowa da Najeriya su, Tarine yawa Najeriya.

 

A bayabayannan dai an dawowa da Najeriya Dala Miliyan 311 daga kasar Amurka inda kuma aka sake gano wasu tarin kudin na Abacha da ake magana akansu a kasar Ingila.

 

Masana sun yi kiyasin cewa tsohon shugaban kasar ya saci kudi da suka kai Dalar Amurka Biliyan 5.

 

A wata kididdiga da jaridar the Cable ta yi, ta gano cewa daga shekarar 1998 zuwa yanzu an kwato dala Biliyan 3.624 na Abacha daga kasashen waje.

 

A hirar da yayi da jaridar TheNation, Buba Galadima ya bayyana cewa yana daya daga cikin yaran Abacha.

 

Kuma a wancan lokacin shine yake kula da hukumar tasoshin ruwa ta Najeriya kuma duk wata maganar shige da ficen kaya a kasarnan hadda maganar Danyen Mai shine ke kula da ita.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Yace to dan haka yana da ta cewa akan mulkin Abcaha. Yace Muammar Gaddafi na Libya da Saddam Hussein na Iraqi ne a wancan lokacin suka baiwa Abacha shawarar kai wasu kudi kasashen waje saboda takunkumin da kasar Amurka tace zata sakawa Najeriya.

 

Yace sun bashi shawarar kai kudin da a kalla zasu rike Najeriya na tsawon watanni 6 koda an saka mata takunkumin.

 

Yace amma wasu nata magana kan Abacha bisa Jahilci. Yace amma dalilin haka shine mulkin Dimokradiyya ake, kowa nada damar ya fadi abinda yake so.

 

Yace shima a yanzu raayinsa ne yake fada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.