Gwamnagin shugaba Buhari ta bayyana cewa yawan biyan kudin fansa da mutane keyi ne yake cigaba da taimakawa masu yin garkuwa da mutane a kasar.
Hadimin shugaban kasa, Garba Sheh ne ya bayyana hakan a ranar litinin yayin daya ke ganawa da manema labarai kan siyasa.
Inda yace gwamnatin Buhari ta cika duka alkauran data yiwa ‘yan kasa na samar da tsaro tattalin arzikin kasar bakidaya.