fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Kudu ma za ta toshe man Fetur zuwa Arewa>>Fani-Kayode

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa kudu zata hana man fetur zuwa arewa, idan jihohin arewa suka dakatar da samar da abinci zuwa kudu.
Akwai rahotanni da ke cewa wasu ‘yan arewa sun yanke shawarar dakatar da safarar kayayyakin abinci, ciki har da shanu zuwa yankin kudancin Najeriya.
Wannan, an tattara shi ne sakamakon rikice-rikicen da ke tsakanin ‘yan kudu da’ yan arewa, musamman rikicin kasuwar Shasha a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo da kuma rikicin makiyaya da manoma a sassa daban-daban na yankin.
A cewar Fani-Kayode, idan arewa ta toshe kayan masarufi zuwa kudu, kudu ma a hakan zata hana arewa samun mai, da kayayyakin da aka tace da kudin mai.
Tsohon Ministan na Sufurin Jiragen ya fadi haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a daren Asabar.
“An kira shi dokar ramuwa. Karka taba fara rawa ba zaka iya gamawa ba! “

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Duminsa: Sakataren OPEC, Muhammad Barkindo ya rasu

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.