fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Kudurin dokar da zai kara wa karatun allo kima

Kudurin dokar ya nemi a kafa hukumar da za ta dinga kula da tsangayoyi da almajirai da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya musamman a jihohin da ke arewacin kasar.

A yanzu haka kudurin ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan kasar.

Manufar kudurin ita ce samar wa masu karatun allo daraja da hanyar dogaro da kai ta yadda al`umma za ta daina kallonsu a matsayin jahilai saboda ba su yi karatun boko ba.

Hon Shehu Kakale shi ne ya gabatar da kudurin ya kuma shaida wa BBC cewa babban burin  wannan hukumar shi ne ta samar da matsayi da kima da mutunci ga karatun almajirci da tsangaya da makaruntun allo a Najeriya.

‘’Ba  zai yuwu a ce  wanda zai iya karatu da rubutu da Larabci ko ajami ko ya haddace Al’kur’ani sannan a ce mi shi jahili ba. ”

‘’Ko kuma dan Najeriya wanda ke Kudu yana sana’oinsa kan harkar spare part na mota ko kuma  harkar kayan sawa wanda ‘yan Kudu ke yi  duk tarin ilimin shi idan bai iya  Turanci ba ko A B C D a ce mai jahili ba.’’

Sannin luggar turanci ba shi kadai bane tsarin ilimin ba

Dan Majalisar ya ce gyara ne ake son a yi  ga tsari na Turawan mulkin mallaka yadda aka fi ba tsarin ilimin boko fifiko  a kan wasu tsaren-tsaren karatu.

 Ana ganin sabuwar hukumar za ta kara bayar da matsayi da kima ga harkar ilimin tsangaya a cewar Hon Kakale:

 ‘’Wannan hukumar za ta bayar da matsayi da kima da takardar shaidar mataki-mataki ga duk wani mai ilimi ko da ilimi ne na fasaha da iya dogaro da kai”, in ji shi.

A baya gwamnatin Goodluck Jonathan ta aiwatar da tsari makamancin wannan inda ta samar da makaruntun almajirai  a sassan Najeriya  domin ta inganta harkar karatun tsangaya.

Sai dai dan Majalisar Wakilan ya ce akwai banbanci sosai tsakanin wannan  tsari da na baya.

‘’A  zagayawar da na yi da kaina a arewacin Najeriya inda na hadu da malamai da alarammomi da hafizai da sauran masu ilimi  a wannan sashin, abin da  ya kawo tangarda a wancan lokaci shi ne  ba a tuntube su yadda ya kamata ba  ta yadda za su san menene bukatarsu amma muhimin abu a wannan doka shi ne bai wa tsarin ilimi  na karatun allo  kima da matsayin da takardar shaida da ta kamace shi.’’

Dan majlisar na son ya sauya tunanin da ake yi a a kan cewa tsarin boko shi ne kawai ilimi saboda a cewarsa abin da duniya take ciki yanzu tsarin ilimi daban da tsarin lugga.

‘’ Yanzu abin da ake yi a Najeriya a tsarin ilimi gaba daya an dauki sanin luggar Turanci shi ne ilimi kuma ba haka ba ne, kasashen duniya da dama ba su Turanci,  yarensu suke yi.”

Sai dai wannan yunkurin na zuwa ne dai dai lokacin da  gwamnonin wasu jihohi  ke neman a soke tsari na yawon almajirai wanda  wani abu ne da ake ganin zai iya cin karo da kudurin  amma dan Majalisar Wakilan ya ce mafi yawancin jihohin  sun fara aikin kafa hukuma irin wannan.

A cewarsa  a jihar Sokoto an fitar da wani kundi  na inganta karatun allo, almajirci da tsangaya a jihar domin ya zo dai dai da tsarin karatun Indonesia.

 Haka kuma  jihohi irinsu Kano da  Borno  da Gombe da Katsina da Yobe suma suna aiki tukuru wajen bai wa tsarin ilimin allo matsayi da kima da ya kamace shi.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *