fbpx
Sunday, June 26
Shadow

“Kullun APC kara karbuwa take a Najeriya”>>Buhari ya taya Oyebanji murnar lashe zaben gwaman jihar Ekiti

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa bayan dan takarar jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji ya lashe zaben gwamnan jihar Eikiti.

Inda shugaba Buhari yace a kullun APC kara samun karbuwa da nasara takeyi a Najeriya, kuma yana fatan Oyebanji zai jajirce sosai a mulkin nasa.

Buhari yace Oyebanji yana kishin Ekiti dama jam’iyyarsu ta APC bakidaya kuma ya cancanci wannan nasarar daya yi.

Oyebanji ya lashe zaben ne da kuru’u 187,057 sai dan takarar SDP Segun Oni ya biyo bayansa da kuru’u 82,211 sa na PDP Bisi Kolawole yazo ba uku da kuru’u 67,457.

Leave a Reply

Your email address will not be published.