Tauraron fina-finan kasar Indiya, Akshay Kumar ya bayyana cewa a kullun yana shan Fitsarin saniya dan neman tsari daga cututtuka.
Dan shekaru 53 ya bayyana hakane inda yace Fitsarin shanun yana matukar taimakawa wajan yaki da cututtuka ciki hadda Coronavirus/COVID-19.
Mutane da dama a India ciki hadda ‘yan Siyasa sun dauka cewa Fitsarin shanun na maganin cutar Coronavirus duk da cewa Likitoci basu tabbatar da hakan a kimiyyance ba.
Akshay ya bayyana hakane a hirar da yayi da dan jaridar Ingila, Bear Grylls