fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Kullun inawa mutanen da matsalar tsaro ta shafa Addu’a amma fa ku sani ba Najeriya ce kadai ke fama da matsalar tsaro ba>>Shugaba Buhari

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan wallafar da Daily Trust ta yi kan matsalar tsaron dake addabar Najeriya, musamman a Arewa.

 

Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu yace lallai Daily Trust ta kawo rahoton gaskiya kuma abinda ta fada haka take.

 

Yace kuma a kullun shugaba Buhari na saka wanda suka samu matsalar tsaron ya rutsa dasu cikin tunani da addu’arsa.

 

Shugaban yace yana baiwa ‘yan Najeriya tabbacin lallai maganin ‘yan Bindiga da ‘yan ta’adda na gaba-gaba cikin abubuwan da yake son cimmawa.

Karanta wannan  Matsalar tsaro: Al'ummar jihata da ido daya suke bacci, cewar gwamna Abiodun

 

Saidai Garba Shehu yace ba Najeriya ce kadai ke fama da matsalar tsaro ba. Yace kwanan nan kasar Amurka tace kasar Mali na iya zama wata sabuwar kasar Afghanistan.

 

Ya kara da cewa, amma fa a sani, matsalar zuwan cutar coronavirus ya kawo matsala sosai wajan yaki da matsalar tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.