fbpx
Monday, August 8
Shadow

Kullun kashe mutanen ku ake ana garkuwa dasu amma ba wannan ne matsalarku ba sai shafukan sada zumunta>>Sanata Shehu Sani ga Gwamnonin Arewa

Sanata Shehu Sani ya caccki gwamnonin Arewa kan kiran da suka yi na cewa a yi dokar da zata saka ido kan shafukan sada zumunta.

 

A jiyane gwamnonin suka fitar da wannan matsaya bayan ganawa da Sarakuna da ‘yan Majalisu da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da shugaban ‘yansanda a Kaduna.

 

Sanata Sani da yake mayar da martani kan lamarin yace kullun ana garkuwa da mutanen ku ana kashesu ana yiwa matansu fyade, da mamaye kauyukansu amma ba wannan ne matsalarku ba sai shafukan sada zumunta.

Karanta wannan  Yadda mutane kusan miliyan guda suka mamaye jihar Nasarawa domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi

 

Northern Governors;Their Kinsmen are being slaughtered daily by Bandits & insurgents,their people are daily being Kidnapped & impoverished by ransom,their women raped & their villages are under siege.Their people live in Fear & Funerals.Yet,Social Media is their problem.

 

Wannan matsaya ta gwamnonin Arewa ta jawo cece-kuce inda da dama sukai ta sukarta.

 

https://twitter.com/ShehuSani/status/1323492888337096704?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.