Sunday, May 31
Shadow

Kuma dai: An kara samun wata daga jihar Nasarawa ta kashe mijinta saboda kishi, ta cire mai mazakuta

Wata mata me shekaru 33, Janet Ekpe ta kashe mijinta, Sunday Ekpe saboda zargin yana lalata da babbar abokiyarta, Hellen.

 

A hirar da TheNation ta yi da matar ta bayyana cewa suna da ‘ya’ya 2 da mijinta kuma a lokacin da suka yi aure suna son juna sosai, suna kwaciyar aure akai-akai amma tana haihuwa ta biyu sai gaba daya ya canja mata.

 

Tace ya daina kula ta kuma ta tambayeshi dalili amma hakan ba ta canja komai ba.

 

Data tsananta bincike sai ta gano she suna soyewa shi da babbar kawarta,Helen.

 

Tace a baya ta rika baiwa kawayenta labarin yanda mininta ya iya kwanciyar aure wanda har suna tsokanarta da cewa ta basu aronshi.

 

Tace da abin ya isheta ne kawai sai ta zuba masa guba a abinci yaci, tana kallonsa tun yana shure-shure har ya mutu.

 

Hakan bai isheta ba, ta je ta samo wuka me kaifi ta yanke masa mazakutarsa ta dora mai a kirji.

 

Da aka yi hira da wani dan uwan marigayin, ya bayyana cewa matar dan uwan nasa ta sha kaimai kuka kuma yana kiranshi ya ja masa kunne amma yaki ji, har ta kai ga haka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *