Gwamnatin tarayya ta sake maye sabon akanta janar din data dora watau Mr. Chukwuyere N. Anamekwe.
Mr. Chukwuyere N. Anamekwe ya maye Ahmad Idris ne da ake zargi da bincike kan sama da fadi da Biliyoyin Naira.
Saidai shima Mr. Chukwuyere N. Anamekwe din EFCC na nemansa. Hakanan kuma rahoton the Natioon yace gwamnatin tarayya bata ji dadin tonon sililin da ya mata ba kan maganar cewa sai ta ciyo bashi take biyan albashi ba.
Kwana bakwai da yin waccan maganace dai aka saukeshi daga mukamin nasa.
Yanzu haka dai gwamnatin tarayya ta fara neman wanda zata nada sabon akanta janar na dindindin.