Lamarin ya farune a karamar hukumar Akinyele dake jihar Oyo inda aka kashe Grace Oshiagwu bayan an mata fyade.
A baya dai an wa Barakat Bello da Azeezat Shomuyiwa irin wannan aika-aika duka dai a wannan karamar hukuma.
Me magana da yawun ‘yansandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan bincike kuma suna kiran da mutanen da suka san wani abu game da lamarin su fito su fada.