Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta sake sakin wasu zafafan hotuna da aka ganta tare da wani abokin aikinta na kudu.
Rahama tace hotunan na wani sabon fim ne da zata yi.
An ganta a hoton kusa da kusa sa abokin aikin nata.


Shigen wadannan hotunan da Rahama Sadau ta saki a baya sun rika jawo cece-kuce sosai musamman a tsakanin masoyanta na Arewa.