Thursday, July 18
Shadow

Kuma Dai: Kungiyar Kwadago, NLC tace zata iya amincewa idan gwamnati ta biya kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa bata nace akan sai gwamnatin tarayya ta biya naira dubu dari biyu da hamsin(250,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi ba.

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa dashi.

Yace a shirye suke su amince da kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin (250,00) a matsayin mafi karancin Albashin.

Gwamnatin tarayya dai bata bayyana matsayar ta ba kan mafi karancin albashin ba.

Karanta Wannan  YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *