fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Kun ci Amanar Almajirai kuma kun mayar da ‘yan Najeriya kamar ba mutane ba>>PDP ta gayawa APC

Jam’iyyar Hamayya ta PDP ta zargi jam’iyya me mulki ta APC da cewa ta ci amanar ‘yan Najeriya da Almajirai bayan ta yi amfani dasu ta cimma burinta na hawa mulki.

 

Akwai dai rahotanni da a yanzu haka suke ta kara fitowa kan yanda gwamnonin jihohin Arewa ke mayar da Almajirai jihohinsu na Asali sannan kuma ana kama motoci cike da Almajiran a wasu jihohin Kudu inda ake mayar dasu inda suka fito.

 

A Sanarwar data fitar ta hannun sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan PDP ta bayyana cewa shugaba Buhari da gwamnatinsa sun lalata duk wani aikin Alherin da ta fara yiwa ‘yan Najeriya a cikin shekaru 5 da suka shafe suna mulki.

 

PDP tace an mayar da ‘yan Najeriya saikace ba mutane ba,harkar tsaro ta tabarbare,Buhari da yace zai jagoranci yaki da Boko Haram amma yanzu yana can a fadarshi yana hutawa.

 

PDP ta bayyana cewa shugaban yana kiran matasan Najeriya ragwaye bayan sune suka hanasu aikin yi.

Karanta wannan  Don Allah ka dauki mace a matsayin abokiyar takararka, matan APC suka roki Tinubu

 

Yace zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ya tona Asirin APC cewa dama can basu da wani tsari na taimakon ‘yan Najeriya, sun hau mulkine kawai su arzuta kansu.

 

Yayi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa su rika taimakon junansu da abinda zasu iya amma dai su lura idan mulkin APC ya kare,, kada su yadda su sake bata damar hawa mulki.

 

A bangarenta,APC ta bayyana cewa An saba jin soki burutsun PDP amma dai abinda yake so su sani shine hakkin maganar Almajirai a hannun gwamnoni yake.

 

A baya dai, Shafin hutudole ya kawo muku labari me taken PDP ta yi ikirarin cewa, Mun gano wasu boyayyun mutane a Gwamnatin Buhari sun shirya tsaf dan sace kudin Abacha da aka dawowa Najeriya

 

Saidai PDP bata bayyana sunan wadannan boyayyun mutane ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.