Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yan Najeriya nada sauran mantuwa, bayan da suke tayin korafe korafe akan matsalar tsaro domin sun mance matsalar tsaron da kasar ke fama da shi kafin ya karbi mulki.
Inda yace gwamnatin shi tayi iya bakin kokarinta akan matsalar tsaro. Buhari ya bayyana hakan ne a taron daya halatta na majalisar zartaswa.
Muhammadu Buhari ya zamo shugaban kasar Najeriya ne a shekarar 2015 karkashin tutar APC kuma yayiwa kasar alkaura wanda suka hada da magance maysalar tsaro.
Amma yanzu kasar na cigaba da fama da matsar tsaro yayin da garkuwa da mutane ya zamo ruwan dare a fadin kasar bakidaya.