Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi bayanin dalilin da yasa ya yafewa tsaffin gwanonin Najeriya, watau Joshua Dariye da Jolly Nyame laifukan satar kudin talakawa.
Tsaffin gwamnonin an kamasu da laifu Dumu-Dumu sannan kuma sun fara zaman kaso na laifukan da suka aikata amma majalisar iyayen kada ta yafe musu laifukan nasu tare da wasu sauran masu laifi sama da 100.
Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda ‘yan Najeriya suka rika mamakin wannan yafiya da akawa gwamnonin musamman a wannan gwamnati dake ikirarin yaki da rashawa da cin hanci.
Saidai kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, kudin tsarin mulki ya baiwa shugaba Buhari ikon yafiya.
Yace sashi na 175 (1) na kudin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ikon yiwa masu laifi Afuwa.
Yace amma ba haka kawai aka yiwa masu laifin afuwa ba, sai da shugaban kasar ya kafa kwamiti kuma kwamitin yayi bincike ya samu hujjoji masu gamsarwa sannan suka baiwa shugaban kasar shawarar yiwa masu laifin Afuwa.
Yace duk da yake yafewa tsaffin gwamnonin dama zai dauki hankulan mutane amma baahi da alaka da siyasa.
Yace kuma hakan ba yana nufin an daina yaki da rashawa da cin hanci a gwamnatin shugaban kasar bane.