Kungiyar gasar kwallon kafa ta Firimiya Lig, Burnley ta kori manajanta Dean Dyche wanda ya kasance yana aiki a kungiyar na tsawon shekaru 10.
Yayin da kuma ta kori mataimakinsa Ian Woan da kocinta Steven Stone da mai horas da masu tsaron ragarta, Billy Mercer.
Kuma a karshe kungiyar tayi masu fatan alkheri tare da yi masu dumbin godiya