fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kungiyar CAN ta kai Wata Ziyara Ga Sarkin Karaye A jihar Kano

Kungiyar CAN ta ziyarci Sarkin Karaye tare da yi masa gaisuwar Sallah

Kungiyar kiristocin Najeriya CAN reshan karamar hukumar Kiru a jihar Kano sun kai wata ziyarar girmamawa Masarautar Kiru tare da yiwa sarkin gaisuwar Sallah a ranar laraba.

Tawagar Kungiyar Kiristocin ta samu jagorancin shugaban reshan kungiyar dake Kiriu Haruna Ishaya.

Da yake Jawabi Mista Ishaya ya bayyana cewa ziyarar wani bangare ne na nuna goyan bayan masarautar tare da yi ma sarkin gaisuawar Sallah.

A jawabin Maimartaba Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar II ya godewa kungiyar, Inda yai kira da fatan samun zaman lafiya da kunciyar hankali a tsakanin Musulmai da kiristan a fadin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.