fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Kungiyar CAN ta zargi El-Rufai da nuna tsatssauran ra’ayin addinin Islama

Kungiyar CAN reshen jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da nuna tsatstsauran ra’ayin addinin Islama.

 

Shugaban kungiyar, Rev. Joseph Hayab Ya bayyana cewa, mutane su yi watsi da kalaman tsohon gwamnan na son musuluntar da Najariya.

 

Yace sun dade suna fadar halin tsohon gwamnan amma a yanzu sun godewa Allah da halinsa ya fito kowa ya gani.

 

Yace goyon bayan da gwamna El-Rufai ya nunawa mulkin musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC yana da wata manufa ce ta son tsayawa takarar shugabancin Najariya nangaba.

 

Yace kuma wannan aniyace ta son raba tsakanin musulmai da kiristocin Najariya.

 

Yace shi El-Rufai fa ko da malaman Addinin Islama ma baya girmamasu, yana yin abinda yake so ne kawai dan cimma burinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *