fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Kungiyar Chelsea tana shirin korar kocinta Frank Lampard

A farkon wannan kakar kungiyar Chelsea tayi kokari sosai yayin da har ake sa ran cewa zata iya lashe kofin Premier League, amma sai dai kungiyar ta koma ta 8 a saman teburin gasar bayan da nasara daya kacal tayi a wasanninta guda shida da suka gabata.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa mai kungiyar Chelsea, Roman Abraham yana shirin korar Frank Lampard saboda kungiyar Chelsea tana bukatar canji bayan da suka sha kashi daci 3-1 a hannun Manchester City.

Kocin Leicester City Bredan Rodgers da tsohon kocin PSG Thomas Tuchel da kuma kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ne ake sa ran zasu mayewa Chelsea gurbin Lampard wanda ya kashe fiye yuro miliyan 220 wurin siyan sababbin yan wasa a kakar bara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.