fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kungiyar dake yiwa Peter Obi yakin neman zabe ta zargi gwamna El Rufa’i da bayar da umurmin hanata yin amfani da babban dakin taro na Arewa House a jihar Kaduna

Kungiyar dake yiwa dan takarar shugaban kasa na Labour Party yakin neman zabe, watau Peter Obi ta koka kan hanata gudanar da taro a jihar Kaduna.

Inda mai magana da yawun kungiyar Sani Saeed Altukry ya bayyana cewa sun biya kudin yin amfani da dakin taron na Arewa House dake layin Rabah a Ungunar Sarki.

Amma kwatsam sai darektan gidan Arewa House din ya kira su ya fada masu cewa ba zasu samu damar yin amfami da dakin taron ba.

Kuma bai fada masu dalili ba haka nan yace masu ba zasu yi amfani dashi ba, amma suna zagin gwamna El Rufa’i ya bayar da umurnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.