fbpx
Friday, July 1
Shadow

Kungiyar Dala’ilul Khairati na kasa ta yiwa kasa addu’ar Neman zaman lafiya a Zariya

Kungiyar Dala’ilul Khairati na kasa ta yiwa kasa addu’ar Neman zaman lafiya a Zariya

Kungiyar salati na dala’ilul khairati na kasa, tare hadin gwiwan wata babban makarantar dala’ilul khairatin, sun gudanar da yima kasa addu’a.”

Kungiyar dala’ilul khairati na kasa sun gudanar da taron yin ma kasa addu’a tare da karrama wasu daga cikin masu basu gudun mawa a garin Zariya jihar kaduna.”

“A wurin babban taronan an jawo hankalin mutane akan su dage da yin ma annabi salati dayin ma kasa addu’a, musamman a wannan lokaci da zamushiga manyan zabuka na kasa, sai dai malamai sunja hankali akan taba daraja fiyayyen halitta, sun ce hakan babu abun da yake jawowa kasa sai bala’i da tabarbarewan arziki.”

Karanta wannan  Labari me dadi: Gwamnatin jihar Kaduna zata dauki malaman firamari guda 10,000 aiki don su maye gurbin guda 2,357 data kora

“Taron ya samu halattan manyan baki dake cikin Nijeriya da wajanta, da suka hada da shugaban salati na kasa da mataimakinsa, da sarkunan salati na jihohi daban daban, da wakilan sarkin zazzau mal Ahmadu Nuhu Bamalli, da ciroman shantalin zazzau da sarkin kasuwan zazzau, da wakilin gwamnan jihar kaduna da manyan malamai.”

“Anyi wannan babban taronne a unguwar magajiya dake cikin birnin zariya a jiya Asabar 22/05/2022.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.