fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Kungiyar Fulani ta Tinubu tayi Allah wadai da kashe al’ummar Najeriya da ‘yan bindiga keyi

Kungiyar matasan Fulani ta AMFON tayi Allah wadai da kashe al’ummar Najeriya da ‘yan binga keyi babu dalili.

Shugaban kungiyar Aliyu Ibrahim Shuaibu ne ya bayyanawa manema labarai hakan bayan sun kammala taro akan marawa Tinubu baya a zaben mai zuwa na shekarar 2023.

Inda yace Fulani sam basa jin dadin kashe mutanen da ‘yan bindiga keyi a fadin kasar nan bakidaya, kuma suna kira ga gwamnatin tarayya tayi kokari ta magance wannan matsalar.

Shuaibu ya kara da cewa ya kamata ‘yan Najeriya su rika taimakawa hukuma wurin basu bayanai akan ‘yan bindigar domin hakan zai taimaka masu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.