Kungiyar ‘yan kwadago ta jihar Ekiti, TUC ta gargardi gwamnan jihar, Kayode Fayemi ya biya ma’aikata albashinsu nan da kwanaki 21.
Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan ta gudanar da babban taro da memboninta a jihar ranar talata.
Inda tace ya kamata ya biya mutane albashinsu kuma ya kara masu matsayi kamar yadda yayi alkawari sanda yake yakin neman zabe a shekarar 2018 domin hakannzai sa su cigaba da son jam’iyyar.
A cikin wannan watan aka gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti kuma APC ta kara yin nasara inda Boidun Oyebanji ya lashe zaben.