fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Kungiyar Gwamnonin Najeriya za su yi wata Ganawa akan cutar COVID-19 Yayinda aka sake buɗe Makarantu

Kungiyar gwamnonin Najeriya a ranar Litinin ta ce za ta hadu a ranar Laraba don tsara hanyar fita daga matsin lamba na dawowar cutar korona karo na biyu yayin da aka sake bude makarantu a duk fadin kasar.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Abdulrazaque Bello-Barkindo, kungiyar gwamnonin ta ce ta firgita da yadda karfin annobar ta biyu ta yadu a duniya”.
Yawan sababbin masu kamuwa da cutar a Nijeriya ya yi tashin gwauron zabi a cikin ‘yan makonnin nan, ganin al’ummar kasar da suka kamu sun tsallake adadin 100,000 na yawan kamuwa da cutar.
Taron na NGF zai kasance na farko ga Gwamnoni a 2021 kuma za’a gudanar dashi ta yanar gizo.
Sauran batutuwan da za a tattauna a taron sun hada da raba kudaden shiga da kuma dokar albarkatun ruwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *