Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya fito fili ya caccaki kungiyarsu ta Inyamurai watau Ohanaeze Ndigbo yace ba zai kara amincewa dasu ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ya fadi zaben fidda gwani na jam’iyyar APC inda yace yawancin Inyamuran basu zabe shi ba face ‘yan jiharsa ta Ebonyi.
Amma yanzu kungiyar ta bashi hakuri tare da sauran ‘yan takararsu da suka fadi, sun ce masu har yanzu akwai kanshin nasara kuma zasu cigaba da mara masu baya.