Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze ta bayyana goyon bayanta ga gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya koma jam’iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa saboda kin amincewar PDP ta baiwa yankin Inyamuran takarar shugaban kasa a shekarar 2023, gwamnan yace zai koma APC.
Sakataren kungiyar, Chucks Ibegbu be ya bayyanawa Punch cewa suna tare da Umahi saboda PDP bata musu Adalci.
Saidai APC tace har yanzu Umahi be sanar da ita a hukumance cewa zai koma jam’iyyar ba amma dai kofarta a Bude take ga kowa.