‘Yan kungiyar Biafra sun saka dokar zaman gida dole ranar talata a kudu masu gabashin Najeriya.
Sun saka wannan dokar ne saboda a ranar kotu zata cigaba da sauraran shari’ar shugabansu, Nnamdi Kanu wanda ke hannun hukumar DSS.
Har yanzu dai dokar su ta zaman gida dole a kowace ranar litinin na cigaba da aiki a jihar, yayin da ake kulle kasuwanni, bankuna da dai sauran su.
Mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyanawa manema labarai wannan maganar a yau ranar litinin.