Mayakan jihadi da ke da alaka da kungiyar IS sun dauki alhakin harin bam din da ya tashi a wata mashaya ta shan giya a kasuwar Mashaya, unguwar Iware a karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba.
An tabbatar da mutuwar mutane shida a harin wanda ya faru ranar Talata yayin da mutane kusan 20 ke samun kulawa a asibitoci biyu.
An tura wadanda suka samu mummunan raunuka zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, FMC, a Jalingo.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da harshen Larabci a ranar Larabar da ta gabata, kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP) ta ce ta tayar da bam din tare da kashe kusan kiristoci 30 tare da lalata mashayar.
A cewar Channels TV, sanarwar da SITE Intelligence da ke sa ido kan ayyukan jihadi a duniya ta fassara, ta ce harin “ramuwar gayya” ne na mutuwar shugabannin kungiyar biyu, ba tare da bayar da karin bayani ba.