fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Kungiyar Izala ta gargadi Sheikh Jalo Jalingo kan hadisin iyayen Annabi

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah ta yi gargaɗi tare da dakatar da ɗaya daga cikin ƴaƴanta wato Dakta Ibrahim Jalo Jalingo daga wani karatu da yake yi wanda yake jawo ce-ce-ku-ce game da iyayen Annabi Muhammad (S.A.W).

A ƴan kwanakin nan dai an sha ganin bidiyo na malamin a shafukan sada zumunta inda yake bayani kan makomar iyayen Annabi, wanda wannan batu ya ja zazzafar muhawara tsakanin ɗaliban ilimi da malamai da mabiya.

A yayin wani taro da ƙungiyar ta yi a sakateriyar ƙungiyar da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ta dakatar da tattauna wannan matsala ko rubutu dangane da ita a shafin intanet domin wannan matsala, lamari ne da ya shafi malamai da ɗaliban ilimi.

A sanarwar da tab wallafa a shafinta, ƙungiyar ta ce yin wannan karatu cikin al’umma ba zai haifar da komi ba sai ruɗani da rashin fahimta.

Kungiyar ta kuma yi kira ga dukkan masu sarrafa shafukan sada zumunta da ke ƙarƙashin ta da su dakatar da yaɗa wannan matsala a shafukan sada zumunta, kuma su janye ta daga shafukansu.

Ƙungiyar ta Izala ta kuma yi kira ga al’ummar Najeriya da su mayar da hankalinsu wajen addu’o’in neman zaman lafiya da tsaro, wanda shi ne babban lamarin da ya dami ƙasar.

Daga cikin malaman da suka halarci zaman har da shugaban ƙungiyar ta Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da kuma sakataren ƙungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe da Sheikh Abubakar Giro Abubakar da kuma shi Sheikh Jalo Jalingon.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.