Kngiyar kare hakkin bil’adama ta SERAP da wasu mutane 185 sun kai karan hukunar dake gudanar da zaben Najeriya ta INEC kotu.
Inda suka shigar da karan saboda hukumar taki karawa masu tin rigistar katin zabe lokaci alhalin amma ta karawa jam’iyyu lokacin gudanar da zabensu na fidda gwani.
INEC ta karawa jam’iyyu kwanaki shida ne daga ranar 3 ga watan yuni zuwa 9 ga watan, amma taki karawa masu yin rigistan katin zabe wanda zai a rufe ranar 30 ga watan yuni bayan sun rufe wanda ake yi a yanar gizo tun 30 ga watan mayu.