fbpx
Monday, May 23
Shadow

Kungiyar kare hakkin bil’adama tayi Allah wadai bayan da Buhari ya bar gwamnan CBN ya tsaya takarar shugaban kasa

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta HURIWA tayi mamakin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya bar gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tsaya takarar shugaban kasa ba tare daya ajiye aikinsa ba.

Gwamnan babban bankin Najeriyar ya sayi fom din APC naira miliyan 100 a ranar juma’a, wanda hakan yasa fusatattun ‘yan kasa suka bukaci ya gaggauta barin ofishinsa idan gar yana son tsayawa takarar.

Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta HURIWA tayi Allah wadai da wannan abin, inda tace a tarihi wannan shine karo na farko da minista ko kuma gwamnan CBN ya tsaya takarar neman shugaban kasa ba tare daya bar ofishinsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.