fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Ya kamata ayi wa makiyaya ragista – Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC)

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta ba da shawarar cewa ya kamata a yi wa masu shanu rajista a kasar domin asan adadin su.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa ya kamata masu shanu su yi rajistar kasuwancin su kamar yadda ake yiwa sauran yan kasuwa rajista.

Ta kuma ba da shawarar cewa ya kamata masu shanu su tunkari bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi don lamunin da za su gina wuraren kiwo.

Shawarwarin na MURIC sun zo ne sakamakon gano cewa mamallakin shanun da suka afka zuwa gidan Farfesa Wole Soyinka dan Kudu ne kuma Bayarabe.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis, 11 ga Fabrairu, 2021 daga daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam, Farfesa Ishaq Akintola.

A cewar sanarwar, “Muna matukar Allah wadai da abin da ya faru yayin da wata saniya ta bata cikin gidan Farfesa Wole Soyinka a Kemta Estate, Abeokuta, a ranar Talata, 9 ga Fabrairu, 2021.

Wannan lamarin ya kara rura wutar rikicin makiyaya da mazauna yankin.

Amma gaskiya ta fara bayyana, domin kuwa mai shanun da suka ɓata a cikin gidan Farfesa Wole Soyinka ya kasance ɗan Kudu ne kuma Bayarabe.

An bayyana shi a matsayin Mista Kazeem Sorinola, dan asalin Ijeun, Abeokuta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *