Kungiyar kiristan Najeriya ta CAN tayi Allah wadai bayan da Inyamurai suka kashe wata mata mai suna Fatima da yaranta guda hudu ba tare da sun aikata laifin komai ba.
Kuma kungiyar tayi kira ga shuwagabannin kungiyar IPOB cewa su daina kashe mutane da manufar cewa suna neman ‘yanci.
A karshe dai kungiyar tayi kira ga gwamnati da hukuma cewa suyi kokari su gano masu kashe mutane babu dalili a kasar nan, kuma su hukunta su.