fbpx
Monday, August 8
Shadow

Kungiyar Kiristocin Arewa ta nesanta kanta da Caccakar da Bishop Kuka yawa Shugaba Buhari

Kungiyar Kiristocin Arewa, NCFN ta nesanta kanta da kalaman caccakar da Fasto Matthew Hassan Kuka yawa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

 

Kungiyar ta fitar da sanarwa jiya, Lahadi a Kaduna daga shugabanta, Rev. Dr. Josiah Nabut inda ta gargadi Bishop Kuka ya daina amfani da cocinsa wajan harkar siyasa.

 

Kungiyar ta bayyana cewa abin takaici ne yanda Fasto Kuka ya bari wasu ‘yan siyasa na amfani dashi wajan cimma manufarsu.

Ta bayyana cewa wadannan kalamai na Kuka sun fito ne daga wasu ‘yan siyasa da yake ganawa dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.