Kungiyar Kwadago ta bayyana cewa zata yi zanga-zangar kwana 1 saboda yajin aikin ADUU da kuma wahalar man fetur.
Kungiyar tace nan da makonni 2 ne zata yi wannan zanga-zangar dan ta tilasta gwamnati ta warware matsalar yajin aikin malaman jami’ar.
Hakanan kungiyar ta yi Allah wadai da yawan samun matsalar rashin man fetur da tace yanawa tattalin arzikin Najariya illa.
Shugaban kungiyar, Ayuba Wabba yayin ganawa da manema labarai yayi Allah wadai da wadannan matsalolin.