Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, NFF zata nada babban kocin Portugal Jose Peseiro a matsayin sabon mai horas da Super Eagles.
Tsohon kocin Barcelona Ernesto Valverde na daya daga kocawan da Najeriya ta tsallake ta zabi Jose.
Kuma tana daf da gabatar da shi a matsayin sabon kocin Super Eagles da zarar ya rattaba hannu a kwantirakinsa.