fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Kungiyar lauyoyi ta kasa zata maka gwamnatin tarayya a kotu kan hana cin ganda

Kungiyar lauyoyi ta kasa ta bayyana cewa zata maka gwamnatin tarayya a kotu muddin ta hana cin ganda a Najeriya.

Jami’in hudda da zama’a na kungiyar Dr. Monday Ubani ne ya bayyana hakan inda yace ganda itace naman marasa karfi domin batada tsada kamar jan nama da kifi.

Saboda haka bai kamata gwamnatin tarayya ta hana cin fatar dabbobin da ake sarrafawa zuwa nama ga talakawa ba.

Gwamnatin tarayya tace zata hana cin gandar domin a habaka kamfanonin leda da sauran kamfanonin daya kamata ace ana sarrafa fatan dabbobin domin samun kudin shiga.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.