Shugaban kungiyar likitocin Najeriya, Uche Ojinmah ya jinjinawa mataimakin shugana kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan amincewa daya yi da likitocin gida aka yi masa tiyata a Najeriya.
Uche Ojinmah ya bayyana hakan ne yayin dayake yiwa Osinbajo fatan samun sauki, inda yace ya kamata sauran ‘yan siyasa suyi koyi dashi su daina fita kasashen waje.
A ranar asabar ne aka yiwa mataimakin shugaban kasar tiyata a kafarsa bayan ya samu rauni a wasan kwallo na squash, kuma anyi nasara a tiyatar da aka yi masa a Ikeja dake Legas.