Wednesday, June 3
Shadow

Kungiyar Madrid da Barcelona sun fara yiwa yan wasan su gwajin cutar Covid-19

Kasar Spain ta kasance daya daga kasashen da cutar Covid-19 tayi kamari kuma a ranar laraba an samu labari cewa gabadaya mutanen da cutar ta kashe sun kai 26,000.

 

 

Yan wasan Madrid da Barcelona sun fara yin gwajin cutar coronavirus a ranar laraba yayin da kungiyoyin la liga suke shirin cigana da atisayi saboda suna sa ran cigaba da wasannin su a wata mai zuwa.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi da dan wasan faransa Antoine Griezmann suna cikin yan wasan da aka yiwa hoto yayin da suke halattar filin atisayin su daya bayan daya a cikin motocin a safiyar ranar laraba, A yan wasan Madrid kuma Eden Hazard  Karim Banzema suna cikin yan wasan da suka halarci gwajin a filin atisayin su.
Ana sanar da sakamakon gwajin cutar ne cikin awanni 48, kuma gwajin yana daya daga cikin sharuddan da aka tsarawa kungiyoyin kafin su cigaba da atisayi. Suma kungiyar Atletico sun yiwa yan wasan su gwajin cutar a ranar laraba.
La liga zasu ba yan wasan damar yin atisayi amma ba a kungiyance ba, Shugaban gasar la liga Javier Tabas ya sanar cewa suna iya bakin kokarin su domin suga cewa an cigaba da buga wasannin gasar a tsakiyar watan yuni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *