Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU ya nemi a hana yaran ‘yan siyasa a kasar waje suma su rika karatu a gida Najeriya tare da ‘yaran talakawa.
Shugaban jami’ar Niger Delta, Kindom Tombra ne ya bayyanawa ‘yan kungiyar kwadago hakan yayin da suke taya su zanga zanga kan yajin aikin da suke yi kuma gwamnati taki waiwayarsu.
Yace idan har aka hana yaran ‘yan siyasa fita kasar waje karatu to ba zasu bari kungiyar malamai ta rika zuwa yajin aiki ba har na tsawon watanni biyar.
Domin yace hakan zai sa su daidaita tsarin karatun Najeriya kuma za a samu cigaba sosai a jami’a da kuma kwalejin kimmiya da fasaha bakidaya.