fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Kungiyar masu motocin Safa sun bukaci yin Sasanci da Hukumar KAROTA ta Jihar Kano kan Umarnin da ta basu na barin Jihar gaba daya

Kungiyar masu motocin safa sun bukaci Yin sulhu da hukumar kAROTA kan Umarnin da ta basu na barin Sabon gari zuwa Tashar Na’ibawa da ke jihar Kano.

Idan zaku tuna mun rawaito muku yadda kotu ta bawa hukumar KAROTA Umarnin aiwatar da Aniyar ta na hana motocin Safa gudanar da ayyukan su a fadin jihar Kano.

Sai dai da Alamu kungiyoyin masu sufurin sun magantu, Inda Lauyan kungiyar Aliyu Yakubu ya Shaidawa kotu a zamanta na ranar Litinin cewa, Kungiyoyin suna kokarin sasantawa da hukumar KAROTA kan Umarnin da a ka basu na komawa tashar Na’ibawa.

Lauyan Ya kuma bukaci kotu data dage karar tare da basu lokaci har su gama sasantawa da hukumar.

Daga bisa ni ne Al’kaliyar Kotun Rakiya Lami Sani ta Amince tare da dage karar har zuwa 25 ga watan Satumba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *