Shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshan jihar Ekiti, Alhaji Adamu Abache, ya umarci mambobinsa da cewa daga yanzu su tona asirin duk wani makiyayi da aka gani yana aikata laifi a jihar.
A cewarsa fallasa bata gari a cikin su shi zai taimaka wajan karawa fulani martaba a jihar.
Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya kan inganta tsaro a jihar da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya shirya ga dukkan kabilun dake jihar.
Hakanan shugaban kungiyar ya haramta amafani da kananan yara wajan kiwan shanu a jihar ya kuma bukaci da gwamnati data taimaka musu wajan yiwa fulani Makiyaya rijista.