Kungiyar dake kare hakkin Musulmai ta MURIC tayi kira ga ma’aikatar jarabawar NECO cewa ta gyara jaduwal dinta na ranar asabar domin ranar yayi daidai da ranar sallar Idi.
Darektan kungiyar,Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan ranar lahadi.
NECO ta saka jarabawar darasin Data Procesing ne daga misalin karfe gom zuwa karfe daya na rana a ranar asabar din.
Amma Akintola ya bukaci ta gyara domin yace itama yasan bada saninta tayi hakan ba.