fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bukaci a sako mata Nnamdi Kanu tunda gwamnati tana gani sarakunan gargajiya sun fara baiwa ‘yan bindiga sarauta

Kungiyar Inyamuran Najeriya ta Ohanaeze Ndigbo ta bukaci shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari usys sako mata Nnamdi Mazi Kanu.

Shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB, Nnamdi ya kasance a hannun jami’am DSS inda suke rukon shi yayin da ake cigaba da gudanar da shari’arsa.

Kuma kungiyar Inyamuran ta bukaci a sako shine bayan sarkin Yandoto na jihar Zamfara ya nada kasurgumin dan bindigar daya tuba, Aleiro a matsayin shugaban Fulani.

Amma gwamnatin jihar ta Zamfaran tuni ta kalubalanci wannan nadin sarautar kuma ta dakatar da sarkin daya yi nadin inda take gudanar da bincike akan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.